Wednesday, 30 September 2015

Buhari Ya Sha Alwashin Tallafa Ma Hukumomin Yaki Da Rashawa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin tallafa ma hukumomin yaki da rashawa na Najeriya.


Shugaban ya bayyana wannan ne a lokacin da aka gudanara da taron National Anti-Corruption Institution in West Africa (NACIWA) a zauren taro na makarantar EFCC dake Karu, Abuja.


buhari i

Shugaba Muhammadu Buhari



Shugaban kasan wanda ya samu wakilci daga Sakataren gwamnatin tarayya, David Lawal ya bayyana cewa hakan ya zama dole domin duk wanda yayi yunkurin yaki da rashawa, toh rashawa zata yake shi.


Yace: “Zata yaki mutum, har ta fara yaka ma. Amma abunda basu sani ba shine, akwai zuciyar yakin, dan haka zamu tabbatar da an samu nasara.


“Ba sai mun jira an tattara duka abunda ake bukata ba, yanzu ne lokacin.”


Shugaban NACIWA Issoufo Boureima ya bayyana cewa akwai bukatar Najeriya ta kauda rashawa a wannan lokacin.


Ya yaba ma Shugaban EFCC na Najeriya inda ya bayyana cewa shi jigo ne wajen kafa NACIWA da kuma karbar bakoncin mutane da yayi daga Jamhuriyyar Benin, Niger, Mali, Togo, Senegal, Cote Voire, Guinea, Burkina Faso da kuma Ghana.


Wakilin Majalisar Dinkin Duniya akan Magunguna da Kwayoyi (UNIDO), Samuel Jaegere ya bayyana muhimmancin tattara bayanai a wanna tafiya.


Yace: “Yanzu da aka samu NACIWA, akwai bukatar a hada gwiwa domin a samun cin nasarar abun da aka sa a gaba.”


Shugaban hukumar hana rashawa ta kasar Siera Leone, Joseph Kamara ya jaddada bukatar dagewa wajen yaki da rashawa.


Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.



The post Buhari Ya Sha Alwashin Tallafa Ma Hukumomin Yaki Da Rashawa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



No comments:

Post a Comment