Sanata Femi Okunrounmu, daya daga cikin shuwagabannin kungiyar Yarabawa ta Afenifere ya bayyana cewa Yarabawa sunyi danasanin zabar Buhari a matsayin shugaban Kasa.
Okunrounmu tsohon mai ba shugaban kasa shawara ne akan taron kasa (National Conference). Ya goyi bayan tsohon Shugaban Kasa Jonathan dominya zarce. Amma Shugaba Buhari ya kada shi inda ya samu Kuri’u Milyan 2 a Kudu Maso Yamma.
A wata ganawa da sukayi da wakilin Jaridar The Punch, Okunrounmu ya bayyana cewa wasu daga cikin zargin da akeyi ma Buhari sun fara tabbata.
Okurounmu yace: “Wannan nade naden da akayi ya nuna cewa Arewa ce zata mamaye kowane bangaren Najeriya. A matsayina na Bayarabe, gaskiya ban gamsu da wadannan nade naden ba.
“Daman ita APC din Arewa tana son mulki ya dawo hannun ta ne. Ita kuma APC din Kudu Maso Yamma tana san canji ne. Daga karshe Arewa tayi amfani da Kudu domin ta shiga fadar shugaban kasa.”
Okunrounmu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya yanzu tana hannun yan Arewa.
“A gwamnati akwai sassa guda 3. Shugaban kasa dan Arewa ne. Shugabannin Majalisar Kasa duk yan Arewa ne, Alkalin Alkalan Najeriya ma dan Arewa ne. Duka wasu wajaje masu karfi duk yan Arewa ne. Duka da cewa muna da Mataimakin shugaban kasa, wannan ba wani abu bane. Domin kundin tsarin mulkin kasa bai bashi wata dama ba ta gudanar da aiki.”
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Yarabawa Sunyi Danasanin Zabar Buhari – Okunrounmu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Post a Comment