Monday, 31 August 2015

Mallakar Adamawa: Rikici Tsakanin Atiku Da Nyako

Akwai alamun rikici tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da kuma tsohon gwamnan Adamawa, Murtala Nyako akan kokarin mallakar Adamawa.



A lokacin zabe, wasu rahotanni sun nuna cewa gwamna Jibrilla Bindow ya samu nasarar lashe zaben saboda taimakon da Nyako ya bashi. Domin kuwa Atiku bai taimaka mashi ba lokacin zaben fidda gwani, Jaridar This Day ta ruwaito.


Nyako da magoya bayan shi su yi tsammanin su zasu hada sama da kashi 90 na gwamnati. Amma kwamishinoni da yawa cikin 22 wadanda Majalisar Jihar ta yarda gwamnan ya nada duk mutanen Atiku ne.


A cikin su akwai Ibrahim Yayaji Mijinyawa, wanda sau 2 yana gwabzawa da Bindow domin neman gwamnan Jihar, da kuma Umar Diya Daware.


A cikin kwamishinonin 22 akwai, tsofaffin kwamishinoni, Muhammad Barkindo Mustafa, Lilian nabe Kayode, da kuma Mata guda 4, Shanti Victoria Shashi, Kaleptapwa Farauta, Fatima Atiku da Lilian Nabe Kayode.


Wasu na ganin cewa gwamnan zaya ba fi ba bangaren Atiku dama a Jihar, ba na Nyako ba wanda ya taimake shi yaci zabe.


Wasu kuma sunce shawara aka bashi akan ya kaucema rikicin Atiku da Nyako domin idan ya dauki bangare, hakan na iya bata  ashi manufar siyasar shi. Wani rikicin siyasa kuma naso ya kara barkewa tsakanin gwamna Bindow da shugaban ma’aikatan shi Abdurrahaman


Abbah.


Abbah yayi sanarwa a kafafen yada labarai cewa gwamnatin Jihar Adamawa zata ware Naira Miliyan 200 domin yin addu’o’i na samun zaman lafiya a Jihar.


Gwamnatin Jihar ta musanta zancen inda gwamnan yayi umurni ga Abbah da kada ya sake yin magan da Yan jarida. Hakan ya sanya ya kai mashi takardar aje aiki.


Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.



The post Mallakar Adamawa: Rikici Tsakanin Atiku Da Nyako appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



No comments:

Post a Comment