Kungiyar kasa ta Inyarumai “Ohanaze ta zargi shugaba Buhari da kin jinin Inyarumai.
A cewar shugaban kjngiyar na Jihar Abia, Dokta Chris Eluemuno “Maganganun da aikatawar Buhari suke nuna haka” Chris yace.
”Shugaba Buhari ba shida wani dalilin yin hakan, hasali ma dai, hakan ne ya Sanya Inyamurai suka ki zaben shi.” jaridar The Sun ta ruwaitu.
Ya fadi hakan ne a wani shiri mai sauna “ku hadu da yan jarida” Na kafar yada labaran jihar ta Abia (ABS).
Shugaban kungiyar kuma ya zargi Buhari da kin nada ko daya daga Cikin Inyamirai a matsayin shugaban soja. Kuma ya nuna rashin jin dadin shi akan yadda Buhari ya kwashi gwamnonin jihohin APC ya tafi dasu Amurka.
Shugaban kuma ya nuna rshin jin dadin shi game da yadda akace Buhari yace zaya saka ma wadanda suka Zabe shi.
Yace: “Babu yadda za’ayi Buhari yayi tsammanin kowa zaya zabe shi. Kuma shirin da yake yi don ya bincike gwamnatin shugaba Jonathan kawai mugunta ce. Ya kamata binciken ya fara tun kan tsohon shugaban kasa Obasonjo.”
Haka zalika wata kungiyar Matasan Inyamirai (NYO) ta gargadi gwamnatin tarayya data bar musguna ma mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu.
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Kungiyar Ohanaze Ta Zargi Buhari Da Kin Jinin Inyamurai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Post a Comment