Friday, 25 September 2015

Kungiya Ta Soki El Rufai Akan Shawarar Daya Ba Buhari

Kungiyar manyan ma’aikata ta Najeriya sun soki Gwamna Nasir El Rufai akan shawarar daya ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan gwamnatin tarayya ta saida kwalin ilimi 104 nata. Ya fadi hakan ne taron tsofaffin talaban Kings Collage dake Legas.



Gwamna Nasir El rufai

Gwamna Nasir El rufai



Kungiyar ta buka ci Buhari ya nisanta kanshi da shawarar da El Rufa’i ya bada akan cewa a saida kwalajin ilimin.


Jaridar Vanguard ta ruwaito cewar Sakataren kungiyar, Alade Bashir Lawal yace kada gwamnati ta saurare shi domin kuwa gwamnatin PDP ma tayi haka a lokacin Obasanjo domin dakushe neman ilimin talakawa.


“Muna ba Buhari shawara ya raba kasnhi da mutane irin su El Rufai domin kuwa suna so su tura shi a samu matsala da mutanen Najeriya.”


El Rufai ya maida hankali akan yadda zaya taimake Miliyoyin Mutanen kaduna wadanda suke yawo akan titi. yayi kokari ya taimaka ma mutanen shi ba wai magana akan abunda zaya sanya ilimin Sakandara ya zama mai tsada ba.


 “A 1966 gwamnatin Balewa ta kafa wadannan makarantu a Warri a Yammacin Najeriya, Sakkawto a Arewacin Najeriya, Okposi a Gabashin Najeriya.


“A yau akwai kwalejojin 104, duka daliban makarantun sunayin kokari a jarabawowin WAEC da NECO idan ka hada su da sauran makarantun dake Najeriya.”


Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.


 



 


The post Kungiya Ta Soki El Rufai Akan Shawarar Daya Ba Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



No comments:

Post a Comment