Monday, 28 September 2015

Wata Kungiya Ta Bukaci A Hukunta Lauyan Saraki

Gamayyar kungiyoyin sakai akan Rashawa (CSNAC) sunyi kira ga Zauren shari’a na kasa (NJC) data hukunta Lauyo shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.



Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki



Kungiyoyin na zargin Lauyan nashi da saka Saraki akan hanyar banza a cikin shari’ar da yake yi a kotun CCT. Jaridar Premium Times ta rahoto cewa, gammayar kungiyoyin sun bayyana wannan ne a ranar Lahadi 27, ga watan Satumba inda shugaban gamayyar, Olanrewaju Suraj.


CSNAC sun bayyana cewa Lauyoyin Saraki, Joseph Daudu, da Mahmud Magai sunyi kuskure inda suka ba Saraki shawara akan kada ya gurfana a gaban Kotun domin suna neman wani umurni daga wata kotun domin hana zaman Kotun.


Sun bayyana cewa: “Mista Magaji ya wanda yake karewa shawara kada yaje kotu inda shi yaje babbar Kotu domin ya domin ya samu umurnin Kotu domin a tsayar da shari’ar.

   

“Shi kuma Mista Daudu shi daya sha alwashin kawo saraki Kotun a ranar Litinin sai bai kawo shi inda yaje Appeal Court domin shima ya samu umurnin kotu akan a hana shari’ar. Sunyi butulci kuma sun saba ma rantsuwar da sukayi a matsayin s na Lauyoyi. Gammayar ta kara jadda cewa dukkanin su ayi masu hukunci domin abunda suka aikata. Muna kira ga kwamitin Lauyoyi da alfarma na zauren shari’a na Najeriya daya hukunta wadannann Lauyoyi guda 2 domin butulcin da sukayi ma rantsuwar da suka yi.

 

“Hakan zaya zama gardai ne ga sauran Lauyoyin aka cewa yin haka ba dai dai ba ne.”


Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.


The post Wata Kungiya Ta Bukaci A Hukunta Lauyan Saraki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



No comments:

Post a Comment