A ranar Alhamis 24, ga watan Satumba, sojojin Najeriya sun bada labarai guda 2 masu dadi akan yakin da yan Boko Haram Inda suka kama inda suke aje Mai da kuma garin Banki.

Yan kungiyar Boko Haram
Daraktan labarai na sojin Kasa, Kanar Sani Usman ya bayyana cewa sun samu nasarar ne ta hanyar wani dan kasa na gari wanda ya sanar dasu. Sojin dibishan ta 3 ne suka tafi inda suka kama inda suke aje Man na Ladu Dumbawa dake a karamar Hukumar Guzamala.
“Idan za’a iya tunawa, yan Boko Haram sunje Gajagere inda suka kama mutane 7 hadda Limamin garin. Wasu masu kokari guda 3 daga cikin su sai suka tsere inda suka kawo ma sojoji rahoton inda wajen yaki.
“Dan haka ne aka yanke masu hanyar samun mansu daga Babangida dake kar Tarmuwa dake Jihar Yobe. Dan haka yanzu an rage masu karfi kuma za’a kauda su kamar yadda ake kokari.
“Yan kasa su sanar da sojoji akan hanyoyin yan Boko Haram, inda suke zama, domin su gama an dakushe su.”
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Sojojin Najeriya Na Cigaba Da Samun Nasarar Yan Boko Haram appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Post a Comment