Tuesday, 1 September 2015

An Harbe Yan Boko Haram Guda 10 A Chadi

An harbe yan kungiyar Boko Haram guda 10 bayan da wata Kotu a N’djamena ta same su da haifin ta’addanci.



An harbe su ne a ranar Lahadi 29 ga watan Agusta a wani gari dake Kilomita 60 daga babban birnin Kasar ta Chadi. An daure su a ranar Juma’a inda ake zargin su da kai hari a kasar a watan Yuli inda sama da mutane 38 suka rasa rayukan su.


A cikin wadanda aka kashe hadda Mahamat Moustafa dan kasar Kamaru wanda ake zargin shi ya shirya harin da aka kai a kasar Chadi a watan Yuli.


Cikin laifukan da aka caje su da su sun hada da, kisan kai, hada kai wajen yin laifi, yin amfani da makma marrassa lasi.


Kungiyar dai ta fara ne a Najeriya wanda daga nan ne ta baza zuwa Kamaru, Chadi da Nijar. Rundunar gamayya dai na nan a Kasar Chadi, N’djamena in da suke fafatawa da kungiyar domin dakile ta.


Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.


The post An Harbe Yan Boko Haram Guda 10 A Chadi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



No comments:

Post a Comment