Gwammar Adam Oshiomhole ya bayyana yadda wani Minstan ya a karsashin gwamnati PDP ya saci Dala Biliyan 6. Jaridar Punch ta ruwaitu.
Gwamnar Adams Oshiomhole wanda tare suka dawo daga Amurka tare da shugaban kasa Buhari ya zargi ministocin tsofuwar gwamnatin da lalata kasar Najeriya.
Ya zargi wani minista da sace sama da Dala Biliyan 6. Yace: “PDP ta lalata kasar na. Ina nufin wannan magana daga bakin wani babban Jami’in harkokin cikin gwamnati Amurka, cewa wani Minista a karkashin gwamnatin PDP ya saci Dala biliyan 6.”
“PDP jam’iyya ce wanda ta shugabanci sace kudinmu, ta lalata duka ma’aikatun gwamnati, ta maida sojoji kamar yan bangar siyasa, ta maida gidan talabijin na kasa kamar Yar abi yariman su, ta lalata jami’an yan sanda masu far in kaya, suka farar ma yan adawa da bi kamar yadda Zomo me Shiga rami, suka lalata kungiyoyin dalibai, da duk wani abuna ka sani. Suka daukaka maganar addini ta zama kamar wani babban sha’anin kasa.”
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Yadda Ministan Jonathan Ya Saci Biliyan 6 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Post a Comment