Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa filin jirgin sama na JFk dake a New York, Amurka, a ranar 24 ga watan Satumba domin taron majalisar dinkin duniya na 70 da za’ayi acan.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhar a New York, birnin Kasar Amurka
Buhari ya samu tarba daga wakiliyar Najeriya a Majalisar Dinkin duniya, Farfesa Joy Ogwu, Babban Sakataren Ma’aikatar harkokin kasashen waje, Ambasada Bulus Lolo, da kuma mai ba shugaban kasa shawara akan tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno mai murabus.
Shugaban kasa zaya yi magana a zauren tattaunawa akan ta’addanci da zaman lafiya wanda shugaban majalisar dinkin duniya Banki Moon da kanshinya gayyace shi zuwan da yayi najeriya.
Shugaban Najeriya zaya tattauna da Barack Obama, Francois Hollande da kuma Bill Clinton. Wannan dai shine zuwan Shugaba Buhari na 2 Amurka.
Zasu tattauna ne akan tattalin arziki, da kuma tsaro sauran shuwagabannin na dun iya.
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Shugaba Buhari Ya Isa New York appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Post a Comment