Bayan zarge zargin da akeyi cewa bai kamata Amina zakari ta shirya zabe ba, mataimakin mai magana da yawun kungiyar Mista Nick Dazang ya musanta wannan ikirarin inda ya bayyana cewa zata iya.
A wata zantawa da sukayi da jaridar The Guardian, Mista Dazanga yace: “Idan ka duba sashe na 153 zuwa na 9 sune sukayi magana akan wannan batu. Sannan kuma kwamishinonin dake a yanzu a hukumar sune zasu fadi yadda za’ayi.
“A yanzu yawan kwamishinonin dake akwai za’a duba. Idan suka yanke wani hukunci akan wani abu toh fa ya yanku.
“Banda sashe na 153 zuwa da 9, ka karanta na 318 sakin layi na 2 na kundun tsarin mulkin kasa na 1999. Ka karanta fassara ta (1)(c)ii na dokar.
”Idan ka duba abunda ya faru lokacin da wa’adin Farfesa Maurice Iwu yayi a hukumar, wani kwamishina sai ya fara ikirarin shine shuga. Hakan ya sanya aka ce bashi bane aka bawa wanda yafi su dadewa a wajen, Solomon Soyebi ya shugabance ta.
“Haka kuma ya faru kafina nada Farfesa Attahiru Jega a 10 ga watan Yuni na 2010. Kwamishinoni 2 suka tafi da hukumar. Suma ne suka samu duk kananan abubuwan da akayi zaben 2011 dasu.
“Babu wata maganar dacewa anan. Abun halatacce ne. Shugaban Kasa nada damar da zaya nada wanda yaga dama idan ya tura Majalisa ta tabbatar da shi.”
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Amina Zakari Zata Iya Shirya Zaben Kogi – Hukumar Zaben Kasa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Post a Comment