Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bada umurni a sanya littafai guda biyu da mai Shari’a Muhammad Bello ya rubuta a cikin jirin littattafan karatun makarantu na Kwalejin tarayya.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a Kaduna a inda aka sake fiddo da littafan da aka rubuta a 1970. Jaridar Vanguard ta ruwaito.
Shugaba Buhari wanda ya samu wakilci daga gwamnan jihar Kaduna El rufai ya jaddada muhimmanci karatun musamman a yanzu da dabi’u keta lalacewa. Sannan kuma ya bada umurni ga ma’aikatar ilimi ta duba taga yadda zatayi domin sanya su cikin littattafan da za’a ringa karantawa a kwalejin ilimi.
Dan siyasan kuma yayi godiya ga duk wadanda suka taimaka wajen sake buga littafan dan su samu shiga tsarin karatun sakandare.
Wasu da suke amfani da kafafen sada zumunta sun bayyana ra’ayoyin su daban daban. Wasu na ganin hakan yayi dai dai, wasu na tsokaci akan hakan.
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Shugaba Buhari Ya Umurci Shigar Da Littattafan Musulunci A Makarantu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Post a Comment