Tuesday, 4 August 2015

Shin an kashe Shekau ne?

Bayan yan kungiyar Boko Haram sun saki sabon Bidiyo inda suke nuna kisan da sukayi ma wani jami’in tsaro da kuma dammarar da suka dauka ta yakar  gwamnatin Buhari, duk ba wannan ba, abunda yan najeriya suka fi Magana akanshi shine wai ina Shekau?


Saboda hare-haren da kungiyar Boko haram ke ta kaiwa a Najeriya, wasu sun fara ganin Shekau a matsayin wani abokin gaba wanda baya mutuwa, wanda ke kashe mutane yana sace masu yara.


Hukumar sojin Najeriya ba sauda daya ba ba sau biyu ba ta sha fadin cewa ta kashe shugaban kungiyar Boko Haram, shekau. A wani shiri da hukumar sojoji tayi a Satumbar data wuce, hedikwatar sojoji ta sake wani yunkurin kashe Shekau a inda har hotunan shi ko kuma mutum mutumin shi data kashe ta nuna. Bayan haka, kafin wata daya Shekau ya fito ya karyata maganar.


A watan maris daya wuce, Shekau ya saki wani Taf inda yake bayyana yin mubayi’a ga tsagerun Daular Musulunci (IS). Masu bincike sun gano cewa lallai Shekau ne yayi wannan Tef din. Amma daga bisani, wanna sabon Bidiyof da suka saki ba’a ganshi ba. Hakan ya sanya ake zargin ya mutu, ko an raunatashi ko kuma ya boye.


The post Shin an kashe Shekau ne? appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



No comments:

Post a Comment