Naij.com ta tattara maku manyan labari guda 10 da sukayi fice a ranar Talata 4 ga watan Agusta. Ku duba domin ku same su.
1. Shugaba Buhari ya amince da nada shugaban hukumar sadarwa ta kasa.
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nada Farfesa Umaru Garba Danbatta amatsayin mataimakin ciyaman, kuma shugaban hukumar kula da sadarwa takasa. Danbatta dai zaya amshi kugerar ne daga Dr Eugene Juwah wadda wa’adin aikin nata ya kare a ranar 29 watan Yuli 2015.
2. Gara in mutu da in bijire ma Buhari – wani sanata da ake zargi.
Sanata Abubakar Kyari yace gara yayi murabus daya shiga cikin gangamin yima gwamnatin shugaba Buhari tawaye.
3. Zargin mutuwar Shekau saboda rashin ganin shi a sabon Bidiyon dakungiyar ta saki.
Wani sabon Bidiyo sa haramtacciyar kungiyar Boko Haram ta saki yinda take nuna kisan da sukayi ma wani soja da kuma cewar su zasu yaki gwamnatin Buhari ya sanya zargin cewa an kashe shugaban kungiyar.
4. Shugaba Buhari ya taya Obama murnar cika shekara 54.
Shugaba Muhammadu Buhari ya taya shugaban kasa Obama murnar cika shekar 54 da haihuwa. Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a shafin shi na twitter inda yace” muna fatan ka kara samun wasu shekaru da cikkaiyar
lafiya”
5. Sojojin sun hana Dalibai 16 yin jarrabawa kuma sun kama su.
Sojojin kasa sun kama Dalibai 16 daga jami’ar Jos inda suka hana su yin jarrabawa. Hakan ya faru ne a ranar Talata 4 ga watan Ogusta.
6. Mi Buhari yake jira wajen kawo karshen Boko Haram?
Mutane da yawa sun zabi shugaba Buhari a zaben daya wuce domin alkawurran da yayi domin kawo karshen Boko Haram. Mi yake jira har yanzu? Bakon mu mai yi mana rubutu Ubaka Chukwuka Maximus ya bayyana ra’ayin shi akan yada za’a kawo karshen abun.
7. Babban bankin Najeriya ya kare martabar Naira.
Babban bankin najeriya ya kare daraja Naira ta hanyar zuba Dala Biliyan 4.9 a watanni 4 na farkon wanna shekara. Kudin dai sun sauko da kashi 14.9. Sun sauko ne daga dala Biliyan 32.24 zuwa ga 29.32 a asusun ajiyar na kasar waje.
8. An kamo wani mai ikirarin Malam ta da yin zinar kwana 3 da wata mata a Legas.
An kama wani mai ikirarin Malam ta a Isolo, Legas, da yin zina da wata mata har na tsawon kwana 4. Matar dai yar shekara 34 da haihuwa.
9. Wata yar wasan kwaikwayo tayi bikin haihuwar Yan Biyun ta a Landan.
Wata yar wasan kwaikwayo mai suna mai suna Taiwo Aromokun tayi bikin haihuwar Yan Biyun ta Landan. Anjoreoluwa and Anjolaoluwa Aromokun. Yan Biyun dai sun samu kyautuka da kauna daga yan uwa da abokan arziki.
10. Wata Uwa ta caka ma danta wuka.
Wata mata mai suna blessing Fred ta caka ma danta dan shekara 7 da haihuwa bayan ya taba al’aurara wata yar magwabtansu mai shekara 5 da haihuwa.
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Manyan Labarai Guda 10 Da Sukayi Fice A Ranar Talata 4 Ga Watan Agusta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Post a Comment