Naij.com ta tattara maku manya labarai da sukayi fice a ranar 3 ga watan Augusta. Ku duba domin ku same su.
1. Yan Boko Haram sun saki sabon Bidiyo inda suke rokon kowa ya shiga yaki da gwamnatin Buhari.
Haramtacciyar kungiyar nan ta Boko Haram ta saki wani Bidiyo wanda ke nuna kisan gilla. Kuma suna shirin fada gwamnatin Buhari.
2. Darajar Naira ta karu saboda Bankuna sun bar ansar Dala.
Darajar Naira ta daga sama sabili da Bankuna sun bar ansar kudaden waje.
3. Sojojin kasa sun kama wani kwamandan Yan Boko Haram kuma sun kubutar da mutane 178 a Bama.
Sojojin Najeriya sun kama wani kwamandan Boko Haram kuma sun kubutar da mutane 178 da suka kama. Hakan dai na cikin kokarin da sojojin Najeriya sukeyi domin su dakile kungiyar.
4. Ngozi ikonjo-Iweala ta canza hali a karkashin Jonathan – Obasanjo.
Obasanjo yace ” Ngozi tayi aikin daya dace a karkashina. Nasan tana da rauni, kuma tana da jajircewa. Tana Bukatar a ringa wai-wayar ta ana duba ta. Yanzu ka duba Ngozi, tayi aiki a karkashina, shin zaka Iya cewa Ngozi daya ce da wadda tayi aiki a karkashin Jonathan?
5. An kama shugaba mai sanya mutane a cikin kungiyar Boko Haram.
Gwamnatin Kasar Chadi ta bayyana cewa ta kama Fana Banaye wanda aka sani da Muhiyat Muhammad a Kasar ta Chadi. Banaye dai shine shugaba mai kula da kai hare-hare a Chadi da Arewacin Kamaru.
6. Fada da ta’addanci: Saraki ya jaddada goyan bayan shi ga shugaba Buhari.
Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya bayyana cewa zaya bawa gwamnatin Buhari duk wani goyon baya da take bukata domin ta samu nasara akan Boko Haram. Ya bayyana hakan ne a ziyarar da suka kai ma gwamnan jihar Borno.
7. Hakumar hana almundahana (EFCC) ta kama shugaban hukumar kula da abinci da magunguna (NAFDAC).
Hukumar hana almundahana ta kama shugaban hukumar NAFDAC mista Paul Orhi. An kama shine saboda zargin almundahana.
8. Amurka zata daga dokar hana saida ma Najeriya makama.
Amurka na shirin daga takunkumin hana saida ma Najeriya makamai. Shugaban kwamitin majalisar Amurka Darell Issa ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da sukayi da shugaban Najeriya da shuwagabannin sojoji a fadar shugaban Kasa.
9. PDP ta rasa kujeru biyu a majalisar wakilai ta kasa.
Jam’iyyar PDP ta rasa kujeru biyu na yan majalisar wakilai ta Kasa. Hakan ya biyo ne bayan da Kotun Tribunal ta Delta ta soke zaben a wani zaman da tayi a warri.
10. Manyan yan wasan kwallon kafa guda 6 sun amshi musulunci.
Akwai da yawa daga cikin yan wasan kwallon kafa wadanda suka amshi addinin musulunci a farko ko kuma karshen rayuwar su. Ku duba safin mu domin kuga manyan guda 6.
The post Manya Manyan Labarai Guda 10 Da Sukayi Fice A Ranar 3 Ga Watan Augusta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Post a Comment