Naija.com ta tattara maku manyan labaran ranar Talata 28 ga watan Yuli data wuce. Ku duba domin ku same su.
1. Yan Boko Haram sun roki Buhari ayi sulhu? Wasu daga cikin sashen yan Boko Haram sun tuntubi shugaba Buhari akan cewa suna so suyi sulhu da gwamnatin Najeriya. Garba Shehu, Babban mai taimakama shugaban kasa akan hudda da jama’a ne ya bayyana hakan a cikin wata takardar manema labarai.
2. Gbajabiamila ya zama shugaban masu rinjaye. A jiya ne Gbajabiamila ya zama shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta kasa. Dogara dai ya kada Gbajabiamila a zaben kakkakin majalisa a tsaben da akayi mai rikici sosai.
3. Matar Saraki ta kawo hayaniya a hedkwatar EFCC. Matar shugaban majalisar dattijai ta kawo hayaniya a Ofishin EFCC Inda ta amsa goron gayyata tare da mutane da yawa. Mutanen da taje dasu sun kutsa kai cikin Ofisoshin na EFCC.
4. Rudanin rishin lafiyar Diezani bayan Oshiomole ya zarge ta da almundahana da Dala Biliyan 6. Akwai alamun karya cikin rashin lafiyar tsohuwar minista Mai Diezani Alison-Madukwe. Tana nuna rashin lafiyar tane domin kaucema bincike. Tun bayan cin zaben Buhari dai mafiya yawa tana can zanne a Landan.
5. Wasikar da majalisar dattawa data wakilai suka karba daga wajen Buhari. Shugaba Buhari ya tura wasiku guda biyu zuwa ga majalisar dattawa data wakilai Inda ya bukace su dasu amince da nadin sabbin shuwagabanni sojoji.
Wasiku dai an karanta sune a zauran majalisoshin a ranar talata 28 ga watan Yuli.
6. Wani babban fasto ya kashe kanshi a cikin kiri-kiri. Wani fasto Destiny Onwundinjo na cocin Divine heaven ministry dake Shasha a Legas ya hallaka kanshi. Abokan zaman gidan yarinshi sukace, faston dai ya kashe kanshi ne saboda daurin da akayi Mashi a gidan yarin har na tsawon shekara 7.
7. Hotunan Whitney Huston da Cristina Bobby zasu baka mamaki. Labarin mutuwar diyar Whitney Huston shekara ukku bayan mutuwar mahaifiyarta zaya baka tausai. Bobbi Cristina an sama ta ba’a cikin hayyacinta ba a kwance cikin kwami wata shidda da suka wuce kamar yadda aka samu mahaifiyarta a 2012. Bata farfado ba dai har mutuwar ta.
8. Diyar tsohon shugaban sojojin ruwa tayi auren kece raini. Diyar tsohon shugaban sojojin ruwa, Jibril Usman tayi auren kece raina. Ta auri Yarima Ibiso Agolia a Abuja. Ita dai an haifeta a garin Fatakwal.
The post Manya Manyan Labarai Na Ranar Talata 28 Ga Watan Yuli appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Post a Comment