Wednesday, 29 July 2015

Buhari Nuna Rashin Jin Dadin Shi Akan Rishin Biyan Malaman Albashinsu

Shugaba Buhari ya bayyana tsananin rashin jin dadin shi game da rashin biyan malaman makaranta albashin su.


A ranara Talata 28 ga watan Yuli, Shugaba Buhari yayi wani taro da manyan shuwagabanni ma’aikatun gwamnati a ofishin ma’aikatar ilmi a Abuja.


Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Shugaban Kasan ya bayyana rashin biyan malaman makaranta albashin su a matsayin “rashin adalci.”


Babban Sakatare ma’aikatar ilimi MachJohn Nwaobiala wanda ya jagoranci tawagar zuwa wajen shugaban kasan ya bayyana ma masu rahoto daga fadar shugaban kasa yadda suka tattauna da shugaban Kasan. Yace: ”Shugaba Buhari baiji dadin rashin bayan albashin malaman makaranta ba. Wasu na bin kudin har na tsawon wata 12.”


Yace, kuma Buhari ya bayyana rashin jin dadin shi game da yadda ake auna darajar Jamio’in Najeriya dana sa’o’insu a sauran kasashe, hakan, ana rashin yinshi yadda ya kamata. Nwaobiala ya bayyana cewa babban kudurin shugaba Buhari yana akan daliban firamare wadanda aka raba da makaranta saboda rikicin da akeyi a kasar Nana.


Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.


The post Buhari Nuna Rashin Jin Dadin Shi Akan Rishin Biyan Malaman Albashinsu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



No comments:

Post a Comment