Peoples Democratic Party (PDP) Jam’iyyar PDP ta nuna goyan bayanta akan yaki da rashawa da kuma Alkalai masu cin rashawa da jam’iyya mai mulki za tayi.
A cikin wasika manema labarai da Sakateran hudda da jama’a na PDP na kasa Olisa Metuh ya sanya ma hannu, yace, APC sun shirya yin yaki da cin hanci, amma ya gargadi APC da kar su dauki masu cin rashawa. Sannan kuma yaba shugabannin APC shawara akan yaki da rashawa.
Cewar Metuh yace: ‘’PDP suna goyan bayan kudurin Gwamnatin Kasa a kan yaki da rashawa a Najeriya. Amma muna fata suyi haka ba tare da sunyi zalunci ba a lokacin yaki da rashawa. Demokratiyya ta samu cindin zama aNajeriya. Muna so ayi komai da adalci ga kowane dan kasa ba tare da kula da siyasa ba, ko addini, ko kabila. Muna kira gare su, ya kamata gwamnantin kasa rufen ido da sababbin Shugabannin kasa tabi shari’a kada tayi ammfani da INEC da yan sanda masu farin kaya (DSS) wajen bin tsohuwar gwamnati.
”Banda shugaba kasa suwaye keda tsarki a Jam’iyyar APC? Da yawa daga cikinsu tsofaffin ministoci ne da kuman gwamnoni masu hannu a rashawoyi da yawa. Sune mafiya hannu cikin rashawoyi a Najeriya. Yanzu da ake yaki da rashawa suna ta kokarin su nuna na Allah ne. Muna ba shugaban kasa shawara a matsayin shi na shugaban jam’i.”
The post Buhari Ne Kawai Mai Tsarki A APC – PDP appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Post a Comment