Tuesday, 28 July 2015

Boko Haram: Shugaba Buhari Zai Je Kamaru

Shugaba Buhari zaya kai ziyara Kasar Kamaru inda zaya tattauna da Shugaba Paul Biya akan yan Boko Haram da suka addabi kasashen biyu.


Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa mai magana da yawun shugaban kasan, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a ranara litinin 27 ga watan Yuli.


Yace: “Shugaba Buhari zaya kai ziyara a kasar Kamaru inda zaya tattauna da shugaba Paul Biya, kuma batun Boko Haram shine babban makasudin tattaunawar. Ziyarar tana cikin tattaunawar neman mafita da akeyi akan ta’addanci yan Boko Haram. Shugaba Buhari da’ yayi niyar zuwa can, amma saboda zuwa taron G7 a Germany sai bai samu ba.”    


Kuma mai magana da yawun shugaban Kasan, Garba Shehu ya tabbatar da hakan. Yace: “Zuwan shi na kwana dayan zaya kara habbaka zumuntar aminci domin a yaki Boko Haram. Idan zaku tuna, ana Sanya tsammani sosai akan Hadin Gwiwar Dakarun Kasashe Wanda ake tsammanin ya kawo karshen ta’addanci a yan kunan. Ba tare da ya bayyana yadda zasu fara ba, shehu yace “dakarun zasu fara aiki a karshen  wannan watan.”


A karshen wannan makon, duka kashashen biyu ne yan Boko Haram suka kaima hari. A Kamaru, wata yarinya yar’ shekara 12 aka Sanya ma Bam Inda ta kashe sama da mutum 18 a Maroua, Kamaru. Wan shekare kuma, a  Damaturun Najeriya, sama da mutum 15 aka kashe.



The post Boko Haram: Shugaba Buhari Zai Je Kamaru appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



No comments:

Post a Comment